Posts

Showing posts from April, 2019

Yau Alhamis likitoci sun ga Shaikh zakzaky

Image
YAU LIKITOCI SUN GA SHAIKH ZAKZAKY Likitoci Daga Kasar Waje Sun Fara Duba Shaikh Ibraheem Zakzaky da matarsa Malama Zeenah a yau Alhamis 25/4/2019. Wannan hoton Shaikh din ne tare da Likitocin nasa a yau Alhamis. Shaikh Ibraheem Zakzaky na tsare tun fiye da Shekaru 3 da suka gabata, duk kuwa da yau fiye da Shekaru biyu da kotun Nijeriya a Abuja tace a sake shi a biya shi diyyar tsarewar da aka masa ba bisa ka'ida ba. A ranar 22 ga Junairun 2019 ne babban lauyan Shaikh Ibraheem Zakzaky, Mr Femi Falana SAN, ya mika bukata ga kotu a kan ta bari a bar Shaikh Ibraheem Zakzaky ya je ya nemi magani a wajen kwararrun Likitoci a waje. Sai kotun ta ba da umurni a zo da Likitocin daga ki ina su duba Shaikh din su ga yanayin jikinsa sai su ba kotu rahoto, sannan ta duba yiwuwar bari a fita da shi ko ai masa magani a nan. Shaikh Zakzaky na fama da rashin lafiya sosai, sakamakon harbin da sojoji suka masa a kafa da hannu da ido, har ya zama ya rasa idonsa guda daya. Haka ma Matarsa...