Yau Alhamis likitoci sun ga Shaikh zakzaky
YAU LIKITOCI SUN GA SHAIKH ZAKZAKY
Likitoci Daga Kasar Waje Sun Fara Duba Shaikh Ibraheem Zakzaky da matarsa Malama Zeenah a yau Alhamis 25/4/2019.
Wannan hoton Shaikh din ne tare da Likitocin nasa a yau Alhamis.
Shaikh Ibraheem Zakzaky na tsare tun fiye da Shekaru 3 da suka gabata, duk kuwa da yau fiye da Shekaru biyu da kotun Nijeriya a Abuja tace a sake shi a biya shi diyyar tsarewar da aka masa ba bisa ka'ida ba.
A ranar 22 ga Junairun 2019 ne babban lauyan Shaikh Ibraheem Zakzaky, Mr Femi Falana SAN, ya mika bukata ga kotu a kan ta bari a bar Shaikh Ibraheem Zakzaky ya je ya nemi magani a wajen kwararrun Likitoci a waje. Sai kotun ta ba da umurni a zo da Likitocin daga ki ina su duba Shaikh din su ga yanayin jikinsa sai su ba kotu rahoto, sannan ta duba yiwuwar bari a fita da shi ko ai masa magani a nan.
Shaikh Zakzaky na fama da rashin lafiya sosai, sakamakon harbin da sojoji suka masa a kafa da hannu da ido, har ya zama ya rasa idonsa guda daya.
Haka ma Matarsa Malama Zeenah Ibraheem, ta na fama da raunin harsasai a yayin da har yanzu akwai wadanda ba a cire su a jikinta ba, har ma ba ta cika iya tafiya da kafarta ba.
Muna fatan Allah Ya baiwa Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya lafiya, ya gaggauta fitowar sa da hallaka duk mai hannu wajen cuta masa.
— Saifullahi M Kabir

Comments
Post a Comment