Yayin da wasu 'yan Najeriya suka shiga rudani dangane da wata jita-jitar cewa za a daina karbar tsofaffin takardun kudi a bankunan kasar nan da dan wani lokaci, wani babban jami'i a daya daga cikin manyan bankunan kasar ya ce mutane sun yi kuskuren fahimtar lamarin. Bincike ya nuna cewa jita-jitar ta sa wasu har karyar da darajar kudadensu suke yi, wadanda suke ganin sun tsufa, inda wasu kan bayar da misali naira dubu daya a ba su kamar naira dari bakwai, ko wani abu na kamar naira dari bakwai ko ma kasa da haka. A wata hira da BBC ta yi da wani babban darakta a daya daga cikin bankunan kasuwanci na kasar, ya ce a umarnin da babban bankin kasar ya ba su babu inda aka ce su sanya wani wa'adi na daina karbar tsohon kudi. Mallam Haruna Musa, na bankin Guarantee Trust Bank, wato GT, ya ce mutane ba su fahimci batun ba yadda ya kamata, shi ya sa ake ta yada wannan jita-jita. Hukuncin kotun Birtaniya zai wa Najeriya illa - Emefiele Sakon WhatsApp zai iya kai mutum gidan ya...