WANENE IMAM HUSAINI KUMA MENENE YA FARU DASHI. WANENE IMAM HUSAINI KUMA MEYA FARU A WAKI'AR KARBALA. @MA'ASUMAH NIG. NEWS UPDATE @ Bayan mutuwar Mu'awiya da kuma fadawar mulki hannun lalataccen dansa Yazidu, sai ya hori gwamnoninsa da su karbi bai'a daga mutane, musamman daga Imam Husaini (a.s.); wannan kuwa saboda irin masaniyar da gidan Umayyawa ke da shi na cewa shi (Husaini) tsayayye ne da ba ya girgiza. Cikin gaggawa Yazidu ya rubutawa gwamnansa na Madina, Walidu bin Utbata, yana horonsa da karba masa bai'ar mutanen Madina gaba daya, musamman Imam Husaini (a.s.). To sai dai Imam (a.s) ya ki amincewa da hakan. Yana mai bayyanawa wa gwamna Walidu cewa: "Yazidu mutum ne fasiki, mashayin giya, mai kashe rai ba bisa hakki ba, mai bayyana fasikanci; iri na ba zai yi mubaya'a ga irinsa ba(1) A gefe guda kuma, Imam Husaini (a.s.) ya bayyana siffofin jagoran da yi masa bai'a ta wajaba, a cikin wasikar da ya aikawa mutanen Kufa, yana mai c...